Album/EP

WATA SABUWA :- Jaruma Daso Ta Bawa Deliget Ɗin Ta Awa 24 Su Dawo Da Kuɗinta.

Fitacciyar Jaruma a masana’antar Kannywood, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Mama Daso ta bayyana bacin ranta cikin wani bidiyo, tana magana da kakkausar murya inda take jan kunnen Daliget da su yi gaggawar dawo mata da kudinta tunda basu zabe ta ba. Kamar yadda jaridar labarun Hausa ta nakalto.

Ga abin da jarumar take cewa a cikin Bidiyon “Daliget ku yi gaggawar dawo min da kudi na naba ku Awa 24 ku dawo min da kudi na tunda kun muna butulci, tun da babu kanwar tsohona a cikinku sabida haka a dawo min da kudina”

Fitacciyar jarumar wadda aka fi sani da Daso a baya ta bayyana cewa ceza ta yi takarar ne domin ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki a yanzu haka.

Amma jarumar har yanzu da rikicin yake faruwa  bata bayyana Jam’iyyar da zata fito Takarar ba, ta bayyana  za ta sanar da jam’iyyar da za ta yi takara a ciki nan gaba kadan.

A baya Jaruma  Daso  ta bayyana haka ne shafinta na Instagram dauke da fostarta, ta bayyana cewa za ta nemi kujerar ne a mahaifarta ta jihar Kano, amma bata sanar da a kowani yanki bane za ta yi takarar.

Ku cigaba da bibiyar mu don samun cikakken labarin nan.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button