Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Umar M Shareef

Umar Muhammad Sharif fitaccen mawakin fina-finan Hausa ne, a hirar da ya yi da Aminiya a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana yadda ya fara waka da irin nasarorin da ya samu da kuma wasu daga cikin kalubalen da ya fuskanta.

Tarihina A Takaice

Assalamu alaikum, sunana Umar Muhammad Sharif,A an haife ni a Rigasa da ke Jihar Kaduna a shekarar 1987. Na yi makarantar firamare da sakandare duk a Rigasa.

Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka
Waka ta fado mini kwatsam da rana tsaka ne, amma a gaskiya ban taba tunanin zan yi sana’ar waka ba, saboda tun tasowata ni dalibi ne, ina karatun boko da na addini, na ma fi ba da karfi a bangaren addini. Silar fara waka kuwa ita ce akwai wata budurwa da nake matukar so da kauna, amma na kasa sanar da ita abin da ke zuciyata.

A gaskiya jin nauyin abin shi ne ya hana ni sanar da ita. Nakan je har kofar gidansu, na aika a yi mini sallama da ita, amma inda gizo ke sakar shi ne da zarar ta fito don ganin wanda ke neman ta, sai na buya, ta gama dube-dubenta daga nan idan ba ta ga kowa ba sai ta koma gida. To na yi hakan kusan har sau uku ba tare da samun damar tsayawa da ita ba. Daga nan wata rana sai na yi ta maza na ce zan ga abin da zai ture wa buzu nadi.

Da na je sai na aika kamar yadda na saba amma sai a wannan karon ba ta fito ba. Na yi ta jira amma shiru kake ji.

To daga nan ne fa kamar wasa sai na fara yin waka a kan halin da na samu kaina ciki. Daga kofar gidansu na fara waka har na isa gida ban daina ba. Haka na yi tayi duk lokacin na tuna da wannan baiwar Allah.

A cikin wannan halin ne sai na samu biro da takarda na rubuta wakar. Akwai wani mawaki Ibrahim Suleiman (Zaki) wanda ya kasance abokin yayana ne.

Kamar wasa da ya ga wakar kuma ya umarce na rera ta. Bayan ya saurari wakar sai ya yaba kuma ya yi min wasu gyararraki, kana ya karantar da ni kabli da ba’adin waka. Daga nan ne fa na fara waka gadan-gadan.

KALUBE

Da farko na fuskanci kalubale daga gida, daga bisani muka fahimtar da iyayenmu. Bayan ba su ga canji daga irin tarbiyyar da suka yi mana ba, sai suka fara sa mana albarka da fatan alheri. Shakka babu addu’o’insu na tasirin sosai a kan nasarorin da muke ci gaba da samu.

WAKOKIN DANAYI

A kalla wakokina za su kai 600
Kundin waka Duka wakokina.

Fitowa a fim Ina fitowa a fim, sannan nakan shirya nawa. Fina-finan da na fito sun hada da: ‘Mahaifiyata’ da ‘Nas’ Mansoor”. Fina-finan da na shirya sun hada da: ‘Ba Zan Barki Ba’ ’Ka So A So ka’ da ’Jinin Jikina ’ ‘Matan Aure’ Jani Muje Da Sauransu.

Mungode damn ziyarar shafinmu mai albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu