Labarai

PDP ta tsayar da Barista Laila Buhari ‘yar takarar sanata a Kano ta tsakiya

Jam’iyyar PDP sun yi zaɓen fida gwani, sun tsayar da Barista Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar sanata a yankin Kano ta tsakiya.

A ranar litinin bayan kammala zaben cikin gida domin fidda yan takara a matakin majalisar dattawa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a jiya Litinin, Barista Laila Buhari, ta samu nasarar zama ‘yar takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya kar kashin jam’iyyar PDP, inda ta samu kuri’u 323 da delegates suka kada.

Kuri’u 331 ne aka kada yayin zaben, inda Laila ta samu 323, yayin da abokin takarar ta, Abubakar Nuhu Danburam, ya samu kuri’u 3, sai kuma ragowar kuri’u 5 da suka lalace (Invalid), kamar yadda yake kunshe cikin takardar sakamakon zabe da jam’iyyar ta fitar.

Jam’iyyar PDP dai a wannan karon ta samu raguwar karsashi ga masu neman takara a matakai daban daban, musamman a jihar Kano, domin kuwa akwai wasu wurare da ba’a samu masu neman tsayawa takara ba, kamar yadda sakataren kwamitin kula da zaben fidda gwani da uwar jam’iyyar ta turo Kano, Sani MB Ahmad, ya bayyana.

A waccen shekarar da ta 2019 da aka yi zabe Batista Laila Buhari ta fito takarar Kano ta tsakiya a Jam’iyyar APDA mai alamar tauraro inda tayi rashin nasara.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button