Labarai

Anyi kira da a sauke babban limamin Abuja Ibrahim Maqari |Fantami Yana shan suka…

Anyi kira da a sauke babban limamin Abuja Ibrahim Maqari, ta inda kuma Professor Isah Ali Ibrahim Pantami yake shan suka a kan Deborah Sameul.

Wanni babban kirintan ya bawa gwamnatin Nijeriya shawara kan su gaggauta sauke babban limamin Abuja Ibrahim Maqari.

hakan ya biyo bayan malamin ya fito yayi magana akan Deborah Sameul wanda tayi ɓatanci ga fiyayyen halita Annabi Muhammad Rasulilahi (S.A.W), inda ya ke cewa abun da samarin suka aikata sun yi daidai.

Hakan ne ya fusata kirintan ya fito yana cewa ayi gaggawar sauke Malam Ibrahim Maqari daga limanaci, saboda yana zuga samari su ringa kashe mutane.

Daga wani ɓangaren kuma mutane suna ta sukar minitan sadarwa kuma babban malamin addinin musulunci a Nijeriya Isah Ali Ibrahim Pantami.

Inda mutane suke cewa Isah Pantami a matsayin shi na babban malamin addinin musulunci, Amma bai fito yayi magana akan kisan Deborah Sameul ba.

Ta inda mutane ke cewa malamin ya fito ya yi magana akan zaɓen da yake taho wa.

Zaku iyya kallon cikakken bayani dangane da wannan batu a ƙasa 👇👇👇

Anyi kira da a sauke babban limamin Abuja Ibrahim Maqari |Fantami Yana shan suka…

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button