Album/EP

KANO :- ‘Yan sanda sun kama wata mota da Bama – Bamai da bindiga AK-47

Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta kama wata mota da bama bamai da bindiga ƙirar AK-47 a cikin motar.

Sanarwa ta fita ne safiyar ranar lahadi daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun sami nasara kama wannan motane biyo bayan bayanan sirri da suka samu a kan shigowar motar jihar.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ƙara da cewa mun sami baya nan sirin ne “A ranar 19/05/2022 muka samu wasu bayanan sirri cewa akwai wata mota kirar Mercedes Benz mai launin toka da ake zargin ta dauko na’urorin hada abubuwan fashewa da bama-bamai.

” cikakken bayanin da muka samu daga bayyana sirin suna nuni da cewa motar zata taso daga jihar Jigawa zuwa cikin birnin jihar Kano.

“Wannan ce ta sanya Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, nan take ya ta da wata tawagar kwararrun jami’ai da suka hada da masu warware duk wani nau’i na bama-bamai da kuma rundunar Operation Kan Ka Ce Kwabo.

“Wani bincike na fasaha da rundunar ta gudanar ya nuna cewa motar makare take da na’urori da kayayyakin hada abubuwan fashewar.

“An kuma samu bindigogi kirar AK-47 guda biyu, kwanson alburusai guda hudu na bindigar AK-47..”

Wannan sune Hotunan da hukumar ‘yan sanda jihar ta bayyana a ƙarkashin SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Sanarwar da SP Kiyawa ya fitar ta ce tuni bincike ya kankama a kan lamarin.

Idan za a iya tunawa, ko a ranar Talatar da ta gabata sai da aka sami fashewar wani abu da ake zargin bam ne a kusa da wata makaranta da ke unguwar Sabon Gari a cikin birnin na Kano, inda aka samu asarar rayuka tara, wasu kuma suka jikkata.

Sai dai a lokacin, ’yan sanda sun tsaya kai da fata cewa wata tukunyar gas ce ta fashe a shagon wani mai walda, ba harin bam ba ne.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button