Jarumar Kannywood Daso ta fito takarar sanata a Kano

fitacciyar jarumar masana’atar shirya fin – finan hausa ( Kannywood) Saratu Gidado ta bayyana aniyarta ta son takarar kujerar sanata a babban zaben 2023 mai zuwa
Jarumar wadda aka fi sani da Daso ta bayyana cewa ceza ta yi takarar ne domin ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki a yanzu haka.
Amma jarumar bata bayyana Jam’iyyar da zata fito Takarar ba, ta bayyana za ta sanar da jam’iyyar da za ta yi takara a ciki nan gaba kadan
fitacciyar jarumar masana’atar shirya fin – finan hausa Kannywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, ta bayyana kudirinta na son takarar kujerar sanata.
Jaruma Daso ta bayyana haka ne shafinta na Instagram dauke da fostarta, ta bayyana cewa za ta nemi kujerar ne a mahaifarta ta jihar Kano, amma bata sanar da a kowani yanki bane za ta yi takarar.
Sai dai ta kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta sanar da jam’iyyar da a karkashin inuwarta za ta yi takara, inda ta bukaci mutane da su taya ta da addu’a.
Jaruma Saratu Giɗaɗo ta wallafa a shafin na Instagram 👇
- “siyasa Barka da safiya ya yan uwana yan Najeriya sannan ina maku barka da karshen mako.
- “Ina burin sanar da abin da kezuciyata da kuma sanar da ku cewa zany i takarar kujerar sanata a jihata ta Kano. Nan ba da dadewa b azan sanar da jam’iyyar.
- “Ina barar addu’arku ce kawai.
- “Manufar: Don ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki. Nagode.
Wannan sune fastocin data wallafa a shafin nata Instagram 👇


Wannan shine shafin jaruma Daso, da abun data wallafa.👇👇
Ku ciga da biyo mu a dan jin Jam’iyyar da wannan jaruam zata fito a ciki.
DAGA :- MANUNIYA