Kannywood

ALAQA Season 2 Episode 8 With English Subtitles

ALAQA Season 2 Episode 8 With English Subtitles .

WALLAHI FARGABAR ABINDA ZAI FARU ACIKIN SHIRIN ALAQA NAKEYI, JI NAKEYI KAMAR A GASKE ZAI FARU

Abubuwa Dai Sun Rinchabe Acikin Wannan Shiri Na ALAQA

A Matsayinmu Na Team Din NAMEER Gaskiya A Ba’a Kyauta Mana Ba 😂

Kasancewar AUDU LULUWA Bashine Wanda HALEESA Takeso Ba Amma Shine Wanda Ya Riga Kama Kafar Wanda Yake Da Ikon Bayar Da Aurenta

ABUN BURGEWA
Abun Burgewa Anan Shine Duk Ikararin Da Dangin AUDU LULUWA Sukeyi Na Wajen Auren HALEESA Ashe Dai Dole Sai Sunbi Hanyar Da Ta Dace, Mafi Yawancin Masu Sauraro Sun Zaci Zasuyi Amfani Da Karfin Iko Ko Kuma Suyi Amfani Da Wata Dama Wajen Ganin Dole Sai Anbasu Auren HALEESA Sai Kuma Abun Yazo Ya Canza

ABUN DA MASU KALLO YAKAMATA SU LURA SHINE:
Duk Inda Mutum Yakai Da Izza Ko Jiji Dakai Dole Akwai Inda Idan Yaje Sai Ya Kwantar Da Kai Kafin Ya Samu Abinda Yake Nema Kamar Yanda Yake Faruwa A Zahiri Haka Acikin Shirin ALAQA Ma Ke Faruwa.

Dama Haka Shirin Film Yakamata Ace Yana Kasancewa, Adinga Nunawa Masu Kallo Abinda Zai Iya Faruwa A Zahiri Ba Kamar Yanda Wasu Masu Shirya Fina-Finai Sukeyi Ba

Sai Kaga Film An Shirya Shi Ta Inda Hankalima Bazai Dauka Ba Balle Ace Har Za’ayi Koyi Da Abinda Aka Gani Acikin Shirin.

JINJINA GA MASU SHIRYA SHIRIN ALAQA

Wani Babban Abun Lura Acikin Shirin ALAQA Shine:
Dukkannin Jaruman Da Suke Cikin Shirin ALAQA Kowannensu Ya Dace Da Fannin Da Aka Sanyashi, Dukkansu Sun Bayar Da Abinda Ake Bukata Daga Kan Jarumai Maza Har Zuwa Mata.

Hakan Ya Samo Asaline Daga Masu Shirya Film Din, Sukan Maida Hankali Akan Jarumai Ganin Sunyi Aiki Cikin Nutsuwa Domin Inganta Sana’arsu.

Da Wannan Kwarewa Nake Kara Yi Musu Addu’ar Allah Ya Kara Musu Basira Da Daukaka Ta Kowani Fanni. Ameen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button