Wasanni

Buhari ka sake bamu dama mu buga wasan duniya D’Tigress

Ƙungiyar ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya ta mayar da martani ga shugaban ƙasa Muhammad Buhari na janye Nijeriya daga duk wani wasan ƙwallon kwando na Duniya.

Sunday Dare, shine ministan matasa da raya wasanni na ƙasa, ya rawaito cewa shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya dakatar da buga wasan ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya, kuma janje war zata dauki tsawon shekara biyu.

Ministan Sunday Dare, ya ce dakatar zai baiwa gwamnatin Nijeriya damar mayar da hankali kan ƙokarin da ake na sake fasalin ‘yan wasa.

Sai dai da suke mayar da martani ungiyar ƙwallon kwando ta matan, a cikin wata sanarwa da suka fitar a shafin su na Twitter ya yin da suke nuna rashin amincewa da dokar da Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya kafa.

“Zamu so a bamu damar bugawa ƙasar mu da muke matuƙar so kuma muke matuƙar son wakilci a wannan gasa mai zuwa, mun yi aiki da tuƙuru don zama 3× Afrobasket Champion, ‘yan Olympics kuma yanzu an albarkace mu da wata dama don cigaba da wakilcin Nijeriya.

” Muna son ƙwallon kwando ta Nijeriya ta cigaba da bunƙasa da samun nasara a kowane mataki, daga wassani na gida, tushe tushen harma mukai matakin ƙasa da ƙasa.

“Sun ƙara da cewa burinsu shine su taka leda da wakilcin Nijeriya cikin Alfahari.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button