Labarai

Ƙasar Saudiyya Ta Bayar Tallafin Naira 131m Ga Marayu 1,960 A Kebbi

Ƙungiyar Masarautar Larabawa ta ƙasar Saudi Arabiya mai suna ( International Islamic Relief Organisation) ta bada naira miliyan 131 ga marayu 1,960 a jihar Kebbi.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu da yake gabatar da shirin a ɗakin taro na gidan Gwamnatin jihar Kebbi, ya nuna jin daɗin sa ga IIRO bisa wannan karamci tare da roƙon a cigaba da gudanar da shirin a cikin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa a raba kuɗaɗen ne ta hannun ungiyar Islamic League a Offishin su na Kaduna.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya samu wakilcin Babale Umar Yauri, sakataren Gwamnatin jihar SSG, ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar mai ci yanzu ta Bagudu ta sanya hannu kan duk wani abu na marayu a jihar.

SSG, ya ƙara da cewa ” Ina so nayi amfani da wannan damar don yin kira ga masu hannu da shuni dasuke cikin al’umma dasu kawo tallafin su don talla fawa marayu don suma su zama kamar Kowa.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button