Labarai

Sojojin sun kashe da’yan ta’adda 42, sun kama 20, sun ceto mutane 63 a Arewa maso gabas

Hedikwatar sojoji ta ce dakarun ta na Operation haɗin kai sun kashe ‘yan ta’adda 43 sun kuma 20 tare da ceto mutum 63 da a ka yi garkuwa da su a ƴan kin Arewa maso gabas cikin makwanni uku.

Mejo.Gen. Bernard Onyeuko shine darakta mai kula da yaɗa labarai ya bayyana cewa ‘yan ta’adda ungiyar Boko Haram 1,627 da iyalansu wanda suka haɗa da maza 331, mata 441 da ƙana nan yara 855, sun miƙa wuya ga sojojin daban – daban tsakanin 1 ga watan mayu zuwa 14 ga watan mayu.

Daraktan yaɗa labarai na tawagar sojojin ya bayyana hakane lokacin da yake zantawa da manema labarai, yake bayyana irin aiki da sojojin suka yi a tsakanin ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan mayu a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ƙara da cewa zuwa yanzu mutane 53,262 suka miƙa wuya tun rara 16 ga watan mayu, Onyeuko ya ce sojojin sun kashe Malam Shehu Wanda shine shugaban ruhin ungiyar.

Yace ranar 14 ga watan mayu sojojin sun yi nasarar kashe Abubakar Sarki kwamandan ‘yan ta’adda da yaran sa a dajin sambisa da ke Yuwe ƙaramar hukumar konduga.

Saboda haka a ya yin wannan farmake farmake da sojojin Nijeriya suka ringa kai wa a, shine ta kai da sun ceto fararen hula 63, sun kashe ‘yan ta’adda 43 tare da kama ‘yan ta’adda 20.

A cewar kwamandan sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar LMGS guda biyu, AK47 guda 21, Ak 56 guda 11, MG guda 22, sun ƙace alburusai 419 na 7.62mm Babita uku.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button