Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Jihar Delta, Sun Kashe Mutum Ɗaya Da Ƙona Motoci Huɗu.

Mutum ɗaya ya mutu bayan da a ke zargin wasu ‘yan ungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra ( IPOB ) ne suka mamaye al’ummar Ugbolu da ke wajen Asaba, babban birnin jihar Delta.

An kuma ƙona mutoci huɗu wanda suka haɗa da manyan motoci ƙirar marsidis guda uku.

Gwamishinan ‘yan sanda na jihar Delta Ari Ali Muhammed, ya tabbatar da hakan ne a yayin da yake ganawa manema labarai na jihar, ya sanar da hakan ne ranar Laraba.

Kwamishinan ya ƙara da cewa wanda ake zargin da ‘Yan ta’addan ne sun tare hanyar Ugbolu inda suka far wa wasu motocin Ɗangote guda biyu, Sun kashe direban ne batan yaƙin in bin umarnin su a kan ya zama ɗaya daga cikin su.

A halin da a ke ciki rundunar ‘yan sandan ta gargaɗi ‘yan ta’adda da su kiyaye idan suka shiga hannun su, Kwamishinan Jihar ya ƙara da cewa jama’ar su kwantar da hankali su kuma bawa jama’a tabbacin kula da zaman lafiya da kula rayu kansu a ko Ina.

Hukumar ‘yan sanda Jihar sun bada tabbacin babu dokar zaman gida a jihar.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button