Labarai

Hukumar NSCDC ta kama mata 2 da laifin safarar mata a Kwara

Jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence NSCDC reshen jihar Kwara ta kama wasu mata guda 2 da laifin safarar ‘yan mata don karuwanci.

Jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence NSCDC reshen jihar Kwara ta hanyar sa ido da bayanan sirin suka sami nasara kama wannan mata guda biyu da ake zargi da safarar mata zuwa wasu Fatakwal zuwa illori babban birnin jihar Kwara, matan suna yen su shine Gift Rita da Joy Samuel.

Kwamandan Civil Defence NSCDC reshen jihar Kwara, da yake gabatar da wanda ake zargi Iskil Makinde, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin abun takaici, yace masu fataucin da ake zargi sun kawo wasu matasa huɗun ‘yan shekara 14,15,16 da 17 a jihar domin yin aiki a wani Hotel don su tara musu kuɗi.

Kwamandan NSCDC reshen jihar ya ƙara da cewa, a halin da ake ji ta bakin mutum biyun da a ke zargi sun ce suna kawo yaran ne don su sami kuɗin su ringa dogara da kansu.

Tuni dai hukumar NSCDC reshen jihar ta miƙa wa ‘yanda a ke zargi zuwa gidan gyaran hali, Kwamandan ya yi kira ga iyayen wa’yan da abun ya shafa dama wanda bai shafaba dasu kula sosai da tarbiyyar ‘ya ‘yan su.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button