Album/EP

‘Yan bindiga sun kai wa matafiya hari a hanyar Abuja zuwa Kaduna

‘Yan bindiga sun sace mutane da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna, in da suka bar motocin matafiyan akan hanya.

‘Yan bindiga da ake zaton masu gar kuwa da mutane ne sun sace matafiya da dama akan fitacciyar hanyar nan ta zuwa Abuja – Kaduna ranar talata.

Wasu daga cikin masu shaidar gani da ido sun shaidawa manaima labarai cewa, abun yafarune misalin na yammacin rana a wani ƙauye mai suna Katari dake hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Suka ƙara da cewa bayan ‘yan bindigar suna gama sace mutanen sun tafi, jami’an tsaro dawa suka ƙaraso gurin domin taimakawa al’umma.

A halin da ake ciki har yanzu babu wani labari daga Gwamnatin jihar Kaduna da kuma jami’an tsaro da suke da alhakin abun, ku tare mu a gaba don samun ƙarin bayani.

DAGA :- Manuniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button