Labarai

Mutum tara 9 ne suka mutu a fashewar iskar gas a Kano

Adadin wanda suka mutum ya ƙaru zuwa tara a fashewar gas a Kano, ta inda aka ringa tsamo gawarwakin daga ɓargunan gini.

Aƙalla mutane tara (9) suka mutu sakamakon fashewar tukunyar gas a Kano ranar talata a unguwar Sabon Gari kan titin Aba kusa da titin kotu, kamar yanda jami’an ‘yan sanda jihar suka sanar.

An ringa tsamo gawarwakin daga ɓargunan ginin daya ruguje kusa da wata makarantar faramare yara.

Kamar yanda jami’an ‘yan sanda suka bayyana sun ce iskar gas ce tayi bundiga, ba kamar yanda mutane suke harshen ba.

Jami’an tsaro sun bada hujjoji kamar haka “Ba fashewar Bom bane fashewar iskar gas ce, kuma iskar gas ɗin ita ce farko wanda aka kashe a gurin.

” Saboda akwai mai walda a kusa da gurin, kuma shine farkon wanda aka ga gawarshi a gurin.

A cewar Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, ya ce lamarin ya farune a akan titin da ake saida dabbobi kusa da wata makarantar faramare yara.

A wata sanarwa da Garba ya fitar, ya yi kira da al’ummar jihar musamman wanda suke a yankin da abun yafaru da su kwantar da hankalin su, saboda ana nan ma’aikata suna aiki.

DAGA :- Manuniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button