Labarai

KANO :- Ganduje ya janye takarar sa ya barwa Barau Jibirin Maliya takarar sanatan Kano ta Arewa.

Bayanai na nuni da cewa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun sami fahimtar juna da Sanata Kano ta Arewa Barau Jibirin Maliya.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibirin Maliya

Daga wasu manya na jikin Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun ce Ganduje da Barau Maliya sun sami fahimtar juna, Kuma Gwamnan Kano Ganduje zai janye wa Sanata Barau Jibirin Maliya takarar sa ta Kano ta Arewa.

A bayane jaridar nan ta Manuniya, ta bayyana muku cewa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sai fom a Jam’iyyar su ta APC na sanatan Kano ta Arewa, wanda shi kuma Sanatan Kano ta Arewa mai ci yanzu yana neman takarar Gwamnan jihar Kano.

Bayan nana Sanatan Kano ta Arewa mai ci yanzu ya fasa fitowa takarar Gwamnan inda yaje ya siyo fom ɗin kujerar kai yanzu ta Sanata don ya maimaita.

Idan Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tin kan zaɓen fidda gwani ya fidda matemakin sa Nasiru Gawuna a matsayin wanda zai gaji kujerar sa, idan Kwamishi nan ƙananan hukumomi mai murabus Murtala Sule Garo a matsayin wanda zai taima kawa Gawuna Wajen neman Gwamnan Kano.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button