Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Mutum 20 A Kaduna

Wasu ‘yan bindiga da aka ce suna da yawa wajen sun kai farmaƙi ƙauyen Kurmin Data da ke dake da tazarar kilomita kaɗan daga Birnin Millennium a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da a ƙalla mutane 20 zuwa wani wuri da ba san inda suke ba.

A cewar ɗaya daga cikin Shugabannin JTF Yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ‘yan bindigar sun far wa Al’ummar ne da misalin ƙarfe 12:16 na safiyar Asabar.

A cewarsa, a cikin mutane 20 da aka yi garkuwa da su da farko, mutane huɗu sun tsere daga hannun masu garkuwar, wanda suka mamaye al’umma da manyan muƙamai.

“Yayin da ‘yan bindigar ke ta harbe – harbe kai tsaye, harsashi ya kashe mutum ɗaya a gidansa, Inji Shi.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button