Album/EP

SOKOTO :- Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Kashe Deborah Sameul

Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Kashe Deborah Sameul Wanda Aka Kashe A Sokoto Akan Ɓatanci Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Rasulilahi S.A.W.

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa tayi kira ga kwantar da hankali zanga – zangar da ake yi a Sokoto saboda kama wa’yanda suka kashe Deborah Sameul a jihar ta Sokoto.

Gwamnonin sun nuna damuwar su a kan lamarin, Ina suka ce bai kamata a ringa ɗaukar duka a hannu ba, haka zalika ungiyar Gwamnonin ta miƙa ta’aziyyar ta ga Iyayen Deborah Sameul da kuma jihar Sokoto.

Sun kuma ja hankalin al’ummar arewacin Nijeriya da su ringa haƙuri da ƙauna da mutunta juna ba tare da la’akari da addinin, ƙabilan ci ko wata alaƙa.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button