Album/EP

Zanga Zanga Ta Ɓarke A Jihar Sokoto, Kan Kama Waɗanda Ake Zargi da Kashe Deborah Sameul

Zanga zanga ta ɓarke a jihar Sokoto, Akan kama waɗan da ake zargin da kashe Deborah Sameul wadda ake zargin ta da aikata da ɓatanci ga Annabi Muhammad Rasulilahi S.A.W

Jaridar Manuniya ta rawaito yanda aka kashe Deborah Sameul ɗaliba a Kwalejin ilimi ta Shehu Shagari dake Sokoto, bisa zargin ta da aikata ɓatan ci ga Annabi Muhammad Rasulilahi S.A.W.

Matasa da ‘yan mata ne suka fito suna zanga zangar da rubuce – rubuce a hannun su kamar haka ” Ku saki ‘yan uwanmu musulmai, mu musulmai ba ‘yan ta’adda bane da dai sauran su.

Hoton zanga zangar Sokoto kan kama wa’yanda ake zargi da kashe Deborah Sameul

Matasan maza da mata sun yi zanga zangar suna ƙona tayoyi a wurare da dama a faɗin jihar inda ya haɗa da Fadar Sarkin Musulmai Alhaji Sa’ad Abubakar wasu kuma ’yan zanga zangar sunyi cinci rundo a fadar Gwamnatin jihar.

Jaridar Manuniya, Da yawan matasan maza da mata suna zanga zangar ne akan suna ganin Sarkin Musulmai Alhaji Sa’ad Abubakar lll yana goyan bayan Deborah Sameul, shi yasa suka je ƙofar gidan sa Suna jefe – jefen duwatsuna.

Gwamnatin jihar Sokoto tasa dukar ta ɓaci a na tsawon awa 24 saboda a shawo kan zanga – zangar .

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button