Labarai

Siyasar Kano :- Shekarau yaƙi amsa gayyatar Buhari saboda ya gano gayyatar ta ƙarya ce

Sanatan Kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau tsohon Gwamnan jihar Kano ya yaƙi amsa gayyatar Gwamna Ganduje, na zuwa Abuja dan tattaunawa da Shugaban ƙasa Muhammad Buhari.

Shekarau :- Bayan gayyatar da Gwamna mai ci yanzu Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa tsohon Gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau har cikin gidan sa a daren ranar juma’a na nufi su tafi Abuja don ganin Buhari game da fitarsa daga APC.

Wasu na kusa da Shekarau sun ce da Darko yayi niyar tafiya Abuja sai ya gano cewa shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da wasu Gwamnonin ne ke son ganawa dashi, Ba Shugaban ƙasa Muhammad Buhari bane yake gayyatar shi ba.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button