Album/EP

Gwamnatin Zamfara ta kasa biyan kuɗin jarrabawar WAEC ta ɗalibai 23,000

Kimanin ɗalibai SS3 23,000 ba za su halarci jarrabawar kammala sakandiri ta yamma cin Afrika ta bana WAEC sakamakon gazawar Gwamnatin jihar Zamfara wajen biyan kuɗin jarrabawar ta WAEC.

Hukumar da take shirya jarrabawar WAEC ta ce za’a hana ɗaliban jihar Zamfara rubuta jarrabawar ne saboda gazawar Gwamnatin jihar wajen biyan kuɗin jarrabawar ga hukumar.

Wata sana wa data fita dag mataimakin magatakarda na jihar, Olufemi Bamigboye ya ce jihar Zamfara na da bashin ku kudaɗen jarrabawar WAEC na shekarar 2019, 2020 da 2021 sama da naira Billiyan ɗaya da dubu ɗari shida bata biya hukumar WAEC ba, kuma ga wannan shekarar ma ta 2022 Gwamnatin jihar bata biya ba.

” A yayin da saura kwanaki huɗu ya rage a fara jarrabawar WAEC ta shekarar 2022 a Nijeriya baki ɗaya, Amma ɗaliban da suka kammala karatu a makarantun Gwamnati a jihar ba su san makomar su ba saboda Gwamnatin jihar bata biya kudaɗen ba.

Olufemi Bamigboye ya ƙara da cewa ” Mun yiwa ɗalibai rijistar jarrabawar a shekarar da ta gabata a sakamakon sa baki da wasu manya na Nijeriya suka yi, cewar Gwamnatin jihar zata da dai – dai tamu ciki harda na shekarar 2019 da 2020 amma har yanzu ba a yi komai ba kuma babu alamar biyan.

” Kuma ya tabbatar da cewa har yanzu ba’a fitar da saka makon jarrabawar WAEC ta shekarar 2019 saboda bashin da ya yiwa jihar yawa kuma ta kasa biyan, Inji Olufemi Bamigboye

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button