Album/EP

SIYASA :- Buhari ya tura jirgin sama Kano ya ɗakko Ganduje da Shekarau domin sulhu

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya tura jirgi sama Kano don ɗakko Gwamnan jihar Kano tare da Sanata Malam Ibrahim Shekarau tsohon Gwamnan jihar Kano zuwa villa don a sasanta su.

A dare yaune Malam Ibrahim Shekarau tsohon Gwamnan jihar da Gwamnan jihar Ganduje zasu tafi Abuja, don tattau nawa da Shugaban ƙasa Muhammad Buhari da iyayen Jam’iyya, don sulhun ta Shekarau da Ganduje.

Mai Magana da yawun Sanata Malam Ibrahim Shekarau Sule Ya’u Sale ya tabbatar wa da manema labarai cewa cikin daren juma’ar nan Shekarau ya karɓi gayyatar shugaba Buhari.

Hakan na zuwa ne yayi da Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya kafa kwamitoci da tuntuɓar magoya bayan sa kan yiwuwar zama ko ficewa daga Jam’iyyar APC, ana sa ranar rahotannin kwamitoci zasu kammala ne ranar Asabar ɗin nan kuma a ranar ake sa ran shekarau zai bayyana makomar sa a siyasar 2023.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button