Album/EPLabarai

Wani Dutse da ya shafe shekaru 400 yana ci da wuta

Wannan wani Dutse ne da ake kira daYanar Dagh” a ƙasar Azarbaijan wanda ya kwashe shekaru 400 yana ci da huta.

Wannan Dutse da yakai kimanin shekaru 400 yana cida wuta wanda ko da ana ruwan sama mai ƙanƙara iska wutar bata daina ci.

Duk wanda yake so yaga wannan wutar ga Bidiyo nan a kasan wannan rubutun mun kawo muku, 👇👇

Wannan shine Bidiyo wutar Yanar Dagh wanda takai shekaru 400 tana ci bata taɓa tsayawa ba koda na minti ɗaya.
Hotunan mutanen da suka je kallon ikon Allah.

Mutane da yawa daga wasu ƙasashen Duniya suna zuwa yawon bude ido wajen wutar Yanar Dagh dake ƙasar Azarbaijan, mutane idan suka je waje suna kwana ki a gurin don kallon ikon Allah.

Idan mutane zukaje suna daɗewa sosai saboda gwamnatin ƙasar Azarbaijan ta gida ƙaton gurin kwanan baƙin da, saboda baƙin da suke zuwa ƙasar yawon bude idon saboda Dutse.

Hoton wani ɓangare daga gurin da mutane suke zama don cin Abinci a gurin wutar “Yanar Dagh “

Kaɗan Daga Cikin Tarihin Dutsen ” Yanar Dagh”

Yanar Dagh Dutse ne dake ƙasar Azarbaijan shi Dutse ne ba kamar ko wane Dutse ba, saboda a kwai kala kalar Duwatsu a duniya kamar Dutse mai aman wuta, Dutse mai fitar da Hayaƙi da Dutse mai fitar da ruwa.

Masu nazarin kimiyya sun ce Dutse Yanar Dagh ya haɗa da tsayayyen iskar gas dake ƙarƙashin ƙasa, Tarihi ya nuna cewa wutar ta farane tin ranar da makiyayin yazo wuce wa ya kuna wutar bisa kuskure har yau taƙi mutuwa.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button