Album/EP

Sojoji sun yi zanga – zangar kan ƙin biyan su Fansho

Wasu sojoji sun yi zanga – zangar rashin biyan su Fansho na tsawon shekara 44 suna aiki tuƙuru, Bayan yanzu shekara su 10 da ajiye aiki.

Sojojin da suka yi zanga – zangar kan shekarar su 10 da ajiye aiki, bayan shekarar su 44 suna wa ƙasa aiki tuƙuru a garin Ibadan na jihar Oyo.

Suna zanga – zangar ƙar ƙashin jagoran cin Cpl. Babawande Philips (rtd) sojojin sun fito suna zanga – zangar akan titinan Ibadan inda suke dauke da kwalaye da rubuce – rubuce da suka haɗa da ” Sojojin da suka yi aiki tuƙuru ga ƙasa tsawon shekaru 44 ba’a biyan su Fansho

Shugaban ƴan zanga – zangar Cpl. Babawande Philips ya bayyana cewa ” An hanamu kudaɗen Fanshon mu na aiki da muka yi tsawon shekaru 44, a aikin mu mun sadaukar da rayukan mu don ƙasar ta zama tsintsiya maduri ɗaya ma ɗauri ɗaya, cewar sa muna so duk al’umma su sani cewa ana yaudarar mu.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button