Labarai

Rashin Tsaro :- ‘Yan ta’adda sun kashe sojoji 6 a jihar Taraba

Hukumar sojojin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar sojoji shida 6 a wani harin kwantan ɓauna ‘yan ta’adda suka kai wa Al’ummar Tati dake ƙaramar hukumar Takum dake jihar Taraba.

A wata sanarwa da kakakin sojojin Birgediya Jabar Onyema Nwachukwu ya fitar, rundunar sojojin ta bayyana cewa dakarunta sun kuma kashe ‘yan ta’adda shida a yayin artabun da suka yi.

Janar Onyema ya kara da cewa Har yanzu ba’a ga wani soja ɗaya ba bayan gama arangamar.

A cewarsa, Sojojin sun sami kiran wayane daga Al’umma akan wasu da ake kyautata zaton ’yan ta’adda ne suka far wa Al’umma Ranar Talata.

Sojojin sunyi ƙaza min fada ta hanyar kwantan ɓauna idan su kai nasara kashe ‘yan bindigar mutum huɗu, Inji Onyema

DAGA:- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button