Labarai

Buhari sunyi zama sirri da Godwin Emefiele Gwamnan Banki

A ranar Alhamis ne aka hangi shugaban ƙasa Muhammad Buhari da Gwamnan Bankin Nijeriya Godwin Emefiele sun yi zama sirri.

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ranar Alhamis a Abuja ya gana a bayan gida da Gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Godwin Emefiele, sunyi ganawar sirri a fadar shugaban ƙasar Nijeriya.

Har yanzu ba’a iya tantance ganawar da shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya yi da Godwin Emefiele har ya zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoton.

Bayan ‘yan jaridun fadar shugaban ƙasa suka yi tsokaci, sai Godwin Emefiele yace bashi da labari a gare su amma nan bada jumawa ba zasu samu labari.

DAGA:- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button