Labarai

Tinubu ya roƙi wakilan APC na Gombe domin samu ƙuri’u

Jagoran Jam’iyyar APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci wakilai daga jahar Gombe da kar su sake su zaɓi wani ɗan takarar a zaɓe fidda gwani idan ba shiba.

Kuma ya basu tabbacin cewa zai gyara musu tsofafin masana’antu, wanda zai samar da aikin yi ga matasa ƙasa baki ɗaya, idan har ya zama shugaban ƙasa.

Inda taron ya gudana ne a gurin taro na gidan Gwamnatin Gombe, kuma ya shaida wa ƴan Jam’iyyar jahar cewa ya gwammace yayi ritaya indai ya fadi a zaɓe fidda gwani da ya koma Jam’iyyar PDP.

Ya ƙara da cewa ” A yau nazo jahar nan ne don neman ƙuri’unku na shugaban ƙasa, ya ƙara da cewa kuna iya zaɓata don cika duk muradan ku kuma nayi imani da kaina inada ƙarfin gwiwa ku zabeni ina rokon ku.

Bola Ahmed Tinubu ya yi Alƙawarin samar da haɗin kai a kasa, ilimi, wutar lantarki, gyara tsofafin masana’antu don samar da aikin yi ga matan ƙasa da sauran abubuwan alkairi da gwamnatinsa tayi ƙudiri.

Tinubu ya baiyana cewa samar da haɗin kai tsakanin matasa zai kawo ƙarshen ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu satar kudi ta yanar gizo da sauran mugayen ɗabi’u da suka da addabi ƙasar nan.

Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Yahaya ya bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin mutum mai iya aiki da kuma cancantar muƙamin da yake nema.

Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu, wanda ya bayyanawa sarkin a matsayin bashi da ƙabila ci kuma shi mai kishin ƙasane da cigaban ta.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button