Labarai

Kwankwaso yace ƙofa a buɗe take da kowa NNPP

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace ƙofa a buɗe take da kowa na Jam’iyyar NNPP ga duk mai sha’awar shiga cikin ta.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fadi hakane lokacin da ake raɗe raɗin cewa tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau, da sauran manyan ƴan Jam’iyyar APC na shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar NNPP.

A jiya talata ne ya tattauna da Freedom Radio Abuja, Kwankwaso ya ƙara da cewa bazai yuba ace iya ƴan Kwankwasiyya ne zasu shiga Jam’iyyar ta NNPP duk mai sha’awa ƙofa a buɗe take.

Cewar Kwankwaso, “Muna maraba da ƴan G-7 saboda suma basa jin daɗin abun da ake musu a jihar Kano.

Yaƙara da cewa matuƙar muna son NNPP ta girma tafi kowa ce Jam’iyya a Nijeriya sai mun ba kowa damar shiga cikin Jam’iyyar NNPP, cewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button