Kannywood

Katsina :- Sai abin da kace muna nan muna biyayya – Lawan Ahmad

Muna nan a Jam’iyyar mu ta APC babu inda zamu je kuma zamu cigaba da biyayya ga shugabannin mu na Jam’iyyar APC, cewar Lawan Ahmad.

Jarumin shirin fina finan hausa Lawan Ahmed wanda a ka fi sani da Umar Hashim a cikin shirin Izzar So, ya ce Suna nan suna jira sai abun da Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari yace shi zasu yi a jihar ta kastina.

Jarum ya wallafa wannan bayani ne a shafin sa na Instagram a yau laraba,

Wannan shine Abun da jarumi Lawan Ahmad ya wallafa a shafin nasa na Instagram.

A shekaran jiya ne Jarumi Lawan Ahmad yake wallafa cewa ya fasa fitowa Takara a jihar ta kastina, baya jaruma ya bayyana cewa zai fito takarar Ɗan malisar tarayya mai wakiltar Bakori L.G.A dake Katsina a Jam’iyyar APC.

Daga baya jarumi ya bayyana cewa ya fasa fitowa takara saboda iyayen sa basa so barema mahaifiyar sa, inda yake cewa indai mutum yana so ya gama da duniya lafiya to yake bin umarnin iyayen sa, yaƙara da cewa Allah yasa hakane alkairi a gurina da masu goyamin Baya.

DAGA:- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button