Album/EP

Za’ayi Wahalar Man Fetur Da Ba A Taɓa Ganin Irin Ta Ba A Nijeriya

Hukumar masu sai da mana fetur mai zaman kanta ta ƙasa, IPMAN tace za’ayi wahalar man fetur da ba’a taɓa ganin irin ta ba a ƙasar nan, matukar ungiyar NMDPRA mai san ya idanu kan harkokin man fetur basu biya kudaden dakon man feturun ba.

Rahotan ya fito daga bakin shugaban hukumar IPMAN na jahar Kano, Bashir Ahmed Ɗan Malam, inda yake cewa manema labarai ranar litinin a Kano yake bayyana musu cewa wahalar man fetur da ƴan Nijeriya suke fuskanta yanzu somin taɓi ne, inda yace bare ma birnin Abuja.

Inda yake bayyanawa manema labarai cewa, rashin biyan kudin dakon wanda kimanin sa ya haura Naira biliyan 500b, yan cewa rashin biyan kudin ne yasa dawa daga cikin dillalan a kaso 100 kaso 5 ne suke iya dakon man fetur din.

Yace sai dai ma’ajiyoyin man dake ƙasar nan suna da mai sosai, amma baza su cigaba da dakko man fetur din zuwa jahohi ba saboda kin biyan su kudaden su Hakan na nema musu illa a kasuwan Cin su.

DAGA :- Manuniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button