Wasanni

Morocco Zata Karɓi Baƙuncin Wasan Ƙarshe Na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai CAF

A ranar 30 ga watan mayu ne Morocco zata karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na gasar cin kofin CAF na shekarar 2022, kamar yanda wani jami’in hukumar Ƙwallon kafar Afrika CAF ya walfa a ranar talata

Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Afrika wato CAF ta karɓi tayin daga Senegal da Morocco, kuma a janyewa Senegal karɓar baƙunci, an baiwa Morocco ƴancin karɓar baƙunci. in ji kakakin hukumar Ƙwallon kafar Afrika

CAF ta bayyana inda ƙasar Morocco ta tanada don buga wasannin, inda za’ayi wasanni sune Agadir, Casablanca, Marrakech, Rabat da Tangiers.

Shawarar buga wasan ƙarshe na gasar cin kofin zakarun turai karo na biyu a ƙasar Morocco, zata bawa Ahly plea mai riƙe da kambun gasar masar kuma zata kara da ƙungiyar Wydad dake Casablanca ta Morocco wasan ƙarshe.

A wasan daf dana kusa dana ƙarshe a ƙarshe makon daya gabata, Wydad ta doke Petro Luanda daci 3-1 a Angola yayin da Ahly ta samu nasara a gida da ci 4-0 Entente daga Algeria.

An shirya wasanni dawowa ne a Casablanca da Algeria a wannan juma’ar da Asabar.

Daga = Manuniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button