Album/EP

Buhari Ya Dawo Abuja Bayan Taron COP-15 A Abidjan Na Ƙasar Kwaddibuwa

A ranar talata ne shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya dawo Abuja bayan halartar shugabanni ƙasashen Duniya a Abidjan na ƙasar Kwaddibuwa

Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammad Buhari a gurin taron kare muhali da a kayi a ƙasar Kwaddibuwa

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari tare da sakatariyyar majalisar ɗinkin duniya Amina Muhammad da ministan muhalin Nijeriya Muhammad Abdullahi a taron kare muhalli da ya ke wakana a Abidjan a ƙasar Kwaddibuwa.

Shugaba Buhari ya bar ƙasar ne ranar lahadi,8 ga watan mayu don halartar taron COP-15.

Majalisar ɗinkin duniya ta shirya taron ne dan makomar kasashe kan Kwararowar Hamada, Fari , Zaftarewar ƙasa, Haƙƙokin al’umma da maido da tattalin arziki ƙasashen duniya.

Shugaba Muhammad Buhari

Buhari a waje taron ya gabatar da bayani kan yanda Nijeriya tace taka rawa waje kare muhalli a wajen taron da aka yi

Shugaba Buhari wanda shi ne ya wakilci Afrika, inda ya samu rakiyar ministan harkokin wajen ƙasar Geoffrey Onyeama; Ministan noma, Dakta Mahmoud Muhammad. Ministan muhalli, Muhammad Abdullahi da ministan albarka tun ruwa injiniya Suleiman Adamu da dai sauran su.

DAGA:- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button