Album/EP

Hanifa :- Wanda Ake Tuhuma Ya Sake Musanta Laifin Kashe Ɗalibarsa

Abdulmalik Tanko, Wanda ake tuhuma da kashe Ɗalibarsa Hanifa Abubakar a karo na uku ya sake musanta zargin da ake masa a gaban kotu.

Hoton :- Abdulmalik Tanko da Hanifa Abubakar, Abdulmalik wanda ake zargi da kashe Ɗalibarsa ƴar shekara biyar

A zaman kotun na baya Abdulmalik ya amsa duk wani laifi da ake zargin sa da aikata wa, amma yazo ya musanta uku daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da su da suka haɗa da garkuwa, azabtarwa da kashe yarinya ƴar shekara biyar.

Amma da aka kara zaman kotu ranar litinin wanda yayi dai dai da 9/5/2022 ” Yana mai cewa shidai laifin da yasan ya aikata shi ne ya yi garkuwa da Hanifa kuma ya nemi kudin fansa naira 100,000.

Ya amsa cewa shine ya sace Hanifa ya kai ta makarantar su ya rufe ta, amma bashi da tabbacin lokacin daya rufe ta babu wanda ya ganshi.

Yanzu dai an kara ɗaga shari’ar zuwa ranar goma 10 ga watan mayu dan cigaba da saura ron shari’ar .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button