Labarai

Buhari kullum da talakawan Nijeriya yake kwana a ransa – Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru yace shugaban ƙasa Muhammad kullum da talakawan Nijeria shugaban ƙasa Muhammad Buhari yake kwana a ransa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a shirin siyasar mu a yau inda ya bayyana nasarorin da aka samu a mulkin Buhari.

Badaru yace ba’a lokacin Buhari aka fara fuskantar matsalar ‘yan bindiga ba, Domin sakakin shugabannin da suka gabata ne yasa ‘yan ta’adda sukayi ƙarfi da yake addabar Nigeriya yanzu.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar Na jihar Jigawa ya kwatanta shugaban ƙasa Muhammad Buhari da babu wani shugaba da a kayi dace a Nijeriya kamar sa.

A yayin tattaunawa a shirin siyasar mu a yau wanda gidan talabijin na Channel yayi, Yace an samu manyan nasarorin a cikin mulkin shugaban ƙasa Muhammad Buhari.

Gwamnan ya ƙara da cewa yanda shugaban ƙasa Buhari yake ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaro da makiyya da manoma abin a jinji na masa ne.

MANUNIYA:- A don gaskiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button