Album/EP

Ganduje ya fidda matemakin sa Nasiru Yusuf Gawuna shine wanda zai gajeshi

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zabi matemakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaji kujerar sa a zaben 2023.

Rahoton daya fito daga jihar sun ce Ganduje ya fidda Nasiru Gawuna a wajen taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar dangane da zaben 2023

Jiga jigai daga Jam’iyyar APC da suka halarci taron sun amince da tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi Murtala Sule Garo a matsayin wanda zai taimakawa Nasiru Gawuna a zaben 2023.

Majiyoyi masu karfi daga wajen taron sun ce sai da jiga jigan Jam’iyyar suka taka rawa matuƙa wajen sa Murtala Sule Garo ya janye daga takarar Gwamna dan ya marawa Nasiru Gawuna Baya.

MANUNIYA:- A don gaskiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button