Labarai

El-Rufai ya nada kwamitin da zai daga darajar KASU dai-dai da zamani

El-Rufai ya nada kwamitin da zai yi  nazarin yadda za a daga darajar KASU domin tayi dai-dai da zamani

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nada kwamitin mutum 7 da zasu tsara sabon jadawali da zai daga darajar jami’ar jihar Kaduna wato KASU domin ganin ta zama zakara a cikin jami’oin Nigeria

Wadanda aka nada din sun hada da  Dr Abba Gumel a matsayin shugaba sai Ibrahim Khalilullahi Zubairu, da Dr. Dahiru Sani da Andrew Bobai Suku da  Mariya Abdulkadir, da Prof. Abu Mallam da kuma Prof. Isa Abubakar.


Cikin abubuwan da kwamitin zai yi sun hada da nazari kan hanyoyi ko matakan da za’abi wajen ganin daga batun koyarwa, tsare tsare da jadawalin KASU ya tafi dai-dai da zamanin da muke ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button