Labarai

Zan kawo gagarumin sauyi a harakar wasannin gargajiya –inji Aminu Bizi

Zan kawo gagarumin sauyi idan na zama shugaban kungiyar wasannin gargajiya –Aminu Bizi

Daga Manuniya

Alhaji Dr. Aminu Aminu Bizi shugaban ya zama sabon zababben shugaban kungiyar masu shirya wasannin gargaji ta Yankin Arewa maso yamma a zaben kungiyar da ya gudana yau Laraba a Kaduna

Alhaji Aminu wanda ya shahara wajen samarwa da matasa ayyukanyi ya lashi takobin ganin ya rubanya wannan hobbasa da yake yiwa matasa idan Allah ya bashi sa’a a zabe nagaba da zasuyi a Abuja.

Yanzu haka dai Aminu na neman takarar shugabancin kungiyar masu shirya wasannin gargaji ta kasa baki daya a zaben da za ayi a makon gobe.

Ya shaidawa Manuniya cewa Ya kuduri aniyar kawo sauye-sauye da zasu bunkusa fannin wasanannin gargajiya idan Allah ya bashi sa’a ya lashe zaben.

“Matasa da dama zasu zama masu dogaro da kai domin zamu bunkasa fannin wasannin gargajiya kama daga langa da, dambe da sauransu. Zamu rika shirya bita da atisaye sannan zamu kirkiro gasar wasannin gargajiya wanda hakan zai bunkasa harakar wasannin gargajiya. Hakazalika zamu horas da yan wasanmu domin ganin Nigeria ta zama zakara a duk fadin duniya” inji Bizi

Bizi ya ce za kuma su hada kai da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin ganin dalibai a makarantu su ma ba a barsu a baya ba a fannin wasannin gargajiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button