Labarai

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Kaduna tayi magana kan jita-jitar rufe hanyoyin sadarwa a jihar

Gwamnatin jahar Kaduna ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa za a rufe hanyoyin sadarwa a jihar Kaduna gobe Laraba.

Manuniya ta ruwaito kakakin Gwamnan jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye ya ce zancen bashi da tushe balle makama.

Ya ce ko kadan babu wani shiri na datse hanyoyin sadarwa a jihar Kaduna a gobe Laraba.  Dama dai anyi ta yada wasu bayanai a yau Talata a shafukan sadarwa dake nuna cewa za a katse layukan sadarwa a jihar Kaduna kamar yadda akayi a jihar Zamfara domin samun damar dakile ayyukan yan ta’adda daji.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button