Labarai

Mazabar Uba Sani sun yi masa gagarumin halacci yau da yaje yin zabe

Yan mazabar Uba Sani sun yi masa gagarumin halacci da yaje yin zabe

Daga Manuniya

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani ya kada kuri’arsa a mazabarsa dake Kawo Kaduna, a zaben kananan hukumomi da ya gudana yau Asabar a jihar.

Manuniya ta ruwaito Uba Sani ya jinjinawa jama’a bisa yadda suka fito domin aiwatar da yancin su ta hanyar yin zabe, ya kuma ce bisa abunda ya gani da kuma bayanan da ya samu sun gamsar dashi cewa zaben yana gudana yadda ya kamata lami lafiya.

Sanatan ya yabawa malaman zaben da kuma uwa uba jami’an tsaro bisa yadda yace suna gudanar da aikinsu a bisa kwarewa a zaben da ya gudana.

“Wannan zabe zai kawo babban cigaba da bunkasar al’amuran a jihar Kaduna ” inji Uba Sani

Manuniya ta ruwaito bayanai daga bisani sun nuna Sanatan ya samu gagarumar nasara a mazabar tasa inda APC ta samu gagarumin rinjaye wanda kuma duk a saboda tasirin sanatan ne wanda tun zuwansa an ga yadda jama’a suka yi dafifi wajen marabtarsa da nuna suna tare dashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button