Labarai

El-Rufai ya lashi takobin yin adalci a zaben Kaduna koda kuwa APC zata sha kayi

El-Rufai ya lashi takobin yin adalci a zaben kananan hukumomin Kaduna koda kuwa APC zata sha kayi

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin tabbatar da anyi gaskiya da adalci a zaben kananan hukumomi da aka gudanar yau a jihar Kaduna ko da kuwa jam’iyyar hamayya zata yi nasara a wasu yankunan a zaben wanda akayi yau Asabar

El-Rufai ya ce ba zai yi irin halin sauran Gwamnoni ko jami’iyyu ba wajen ganin ko da tsiya sun murde zabukan kananan hukumomi domin a cewar Gwamnan wannan zalunci ne da tauye wa jama’a yancinsu da kundin tsarin mulki ya basu na zabar wanda suke so

Gwamnan wanda ke jawabi yau Asabar Jim kadan bayan kammala kada kuri’arsa a mazabarsa dake Unguwar Sarki ya ce ya umurci hukumar zabe ta jihar Kaduna SIECOM su tabbatar sunyi adalci kuma sunyi aikinsu a bisa kwarewa “kuma mun ji dadi yadda akayi amfani da na’urori wajen gudanar da zaben. Kuma ina alfahari da hukumar zabe ta SIECOM domin yadda suka jajruce wajen ganin sun kawo kayan aiki na zamani”

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya kara da cewa ba zamu tursasawa jama’a ba, kowa ya zabi son shi amma kuma ba zamu zura ido ayi mana magudi ba, “Mun bar jama’a su zabi wanda suke so, muna da kwarin guiwa duk mai hankali da tunani yaga ayyukan cigaban da muke yi a jihar Kaduna kuma an ga kokarin da muke yi don haka muna da yakinin zasu bamu goyon baya”

Sai dai jami’iyyar PDP ta sha albashin kada Gwamnan a mazabarsa ta 001 dake Ungwar Sarki, a karamar hukumar Kaduna ta Arewa,  Manuniya ta ruwaito daga Majiyoyi bayan kirga sakamakon zabe da Muhammad Sani, yayi ya ce APC ta samu kuri’u 62 a zaben ciyaman a yayinda PDP ta samu kuri’u 86 daga cikin kuri’u 159 da aka kada.

A zaben Kansila kuma, APC ta samu kuri’u 53 PDP kuma 100 daga cikin kuri’u 162 da aka kada.

Sai dai kawo lokacin kammala wannan rahoton ba a kai ga fadin sakamakon zaben karamar hukumar Kaduna ta Arewan ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button