Labarai

An kashe babban dan Sanata Bala Na’Allah, Kaptin Abdulkarim a gidansa dake Kaduna

An kashe babban dan Sanata Bala Na’Allah, Kaptin Abdulkarim a gidansa dake Kaduna

Daga Manuniya

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewa an je har gida an kashe babban dan Sanata Bala Na Allah, Captain Abdulkarim Bala Na Allah, a gidansa dake Malali a jihar Kaduna.

Majiyar MANUNIYA ta ruwaito cewa an ga gawar margayin a dakinsa a yammacin yau Lahadi. Margayin mai shekara 36 dai matukin jirgi ne kuma bai jima da yin aure ba.

Manuniya ta kuma tattaro cewa an ga gawar mamacin ne a daure a cikin dakinsa, sannan ana zargin maharan sun tafi da mota da sauran kadarorin margayin bayan sun kashe shi.

DailyTrust ta ruwaito cewa mahaifin mamacin Sanata Na Allah, baya kasa a lokacinda abun ya faru amma dai wani hadiminsa Garba Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin. Kuma ya ce tuni sun sanar da hukumar yan sandan jihar Kaduna.

A cewarsa ana zargin maharan sun kutsa gidan margayin ne ta rufin daki kuma har suka shiga dakinsa suka rutsa shi suka kashe shi. Ya ce wani mai gadi ne ya kwarmata ihu bayan ya ankara cewa an wangale kofar gidan mamacin.

Manuniya ta ruwaito tuni an soma shirin yin jana’izar marigayi Mohammed a masallacin Yahaya road sannan za a bizne shi a makabartar Unguwan Sarki dake Kaduna.

Sanata Bala Na’Allah mai wakiltar Kebbi ta Kudu a zauren majalisar tarayya yana da ‘yaya Uku wadanda dukansu matukan jirage.

Babangida Aliyu ya yada rahoton faruwar lamarin inda yace “Innalillahi wa inna ilihir rajiun “

Yanzu muka sami labarin rasuwar Captain Aldulkarim Na Allah. Babban dan Senator Bala IBN Na Allah.  Wanda ake zargin wasu ne suka kashe shi a gidan sa dake Umar Gwandu Road off Gwanja Road Malali.

Za ayi jana’iza a makabartar anguwar sarki kaduna. Allah gafarta masa yasa ya huta”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button