Labarai

Masu garkuwa sun shiga gidan mutuwa sun yi awon gaba da duka masu zaman makoki a Katsina

Rahotanni da dumi-duminsu daga jihar Katsina suna bayyana cewa a daren jiya Talata yan bindiga sun shiga cikin wani gidan makoki a garin Kofa dake cikin karamar hukumar Kusada sun yi awon gaba da gwamman mutane dake zaman ta’aziyya.

Manuniya ta ruwaito wani Madahuru Isah Ibrahim ya rubuta karin bayani a shafinsa na Facebook cewa:-

“Innalillahi wa’innah ilaihir raji’un

Cikin dare’ n nan masu garkuwa da jama’a sun shiga cikin garin Kofa dake karamar hukumar Kusada, jihar katsina, inda suka rufta gidan makoki suka tarkata masu zaman makokin suka korasu daji.

Wannan lamari Allah kafitar da bayin ka cikin aminci….”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button