Labarai

Magidanci mai mata 2 da ya’ya 12 nason a bashi auren diyar shugaba Buhari, Noor

Magidanci mai mata 2 da ya’ya 12 nason ya auri diyar shugaba Buhari, Noor

Daga Manuniya

Wani magidanci mai mata biyu da ‘ya’ya 12 ya nuna muradinsa na son auren autar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Noor.

Mutumin mai suna Bukar A Bukar mazaunin Maiduguri ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa a shirye yake ya aure Noor a matsayin mata ta Uku idan ta amince.

Tun bayan kammala auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari Yusuf Buhari da diyar Sarkin Bichi, Zara Bayero jama’a suka kwallafa ido kan diyar shugaban kasar wacce ta rage da akace sunan ta Noor.

Samari da dama sun yi ca a kafafen sadarwat zamani suna ta nuna sha’awa da muradin soyayyarsu ga autar Shugaban kasar tare da fatan ina ma dai Allah ya kai damo ga harawa.

Sai dai wanda yafi daukar hankali shine na dan Borno wato Bukar ganin cewa har da neman a tayashi addu’ar Allah ya bashi sa’a yayi wuuf da diyar shugaban kasar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button