Labarai

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kashe babban sojan da suka sace a NDA bayan sun nemi fansar N200m

Da Dumi-Dumi: An tsinci gawar Manjo Datong babban sojan da yan bindiga suka sace a NDA Kaduna

Daga Manuniya

Rahotanni daga jihar Kaduna suna bayyana cewa yan bindiga sun kashe babban sojan nan da sukayi garkuwa dashi a makarantar Sojoji ta NDA, Manjo Christopher Datong a yau Talatu.

Kodayake dai ba a tantance gaskiyar labarin ba amma dai Manuniya ta tattaro daga majiyoyi da dama cewa an tsinci gawar babban sojan ne da yammacin yau Talata.

Tun da farko dai bayanai sun nuna yan bindigar sun nemi a biyasu Naira miliyan 200 kudin fansa kafin su sako babban sojan wanda suka sace shi har cikin NDA Afaka a yayin harin da suka kai na daren ranar Litinin.


PMNews ta ruwaito an haifi margayi Datong a garin Pankshin dake jihar Plateau a ranar 4 ga watan Janairun, 1978.

A wasu hotuna da aka yada Manuniya ta ruwaito an ga matarsa da ciki kodayake babu tabbacin hoton sabo ne ko tsoho

Kawo yanzu dai da muke saka labarin babu wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin na gaskiyar cewa an kashe shi ko yana raye

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button