Labarai

DA DUMI-DUMI: An kaiwa kwalejin horas da sojoji ta NDA hari, an kashe sojoji tare da garkuwa da wasu

DA DUMI-DUMI: Yan bindiga sun kai hari kwalejin horas da sojojin ta NDA sun kashe sojoji tare da garkuwa da wasu

Daga Manuniya

Yan bindiga sun kai farmaki cikin kwalejin horas da sojoji dake Afaka (NDA Afaka) inda nan take suka kashe akalla sojoji 2 kana suka jikkata wasu sannan kuma suka tafi da wasu manyan sojoji da ba a tantance yawansu ba.


Wani mazaunin yankin ya shaidawa Manuniya cewa maharan sun kai hari ne a daren jiya Talata inda suka kutsa cikin NDA sanye da kayan sojoji kuma da shigarsu sai suka doshi rukunin gidajen manyan sojoju wato “officers’ quarters” suka kai harin.

Rahotanni sun ce yanzu haka an kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti a yayin da aka tabbatar da sun kashe wani Manjo daya da Squadron Leader kana kuma suka gudu da akalla wani Majo cikin daji.

Majiyar MANUNIYA ta ce nan take sashin bayar da tsaron gaggawa na NDA Quick Response Team, sun kai dauki amma basu samu nasarar kubutarwa ko kama yan bindigar ba.

Kodayake dai kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan adadin baranar da yan bindigar sukayi to amma Rahotanni sun ce an tura dakarun sojin sama da kasa sun bazama cikin daji domin kubutar da sojojin da aka sace.

Kwalejin horas da Sojoji ta NDA dai tana kusa da kwalejin koyar da aikin gona ta Federal College of Forestry Mechanization Afaka, a cikin karamar hukumar Igabi makarantar da yan bindigar suka sace dalibai 39 a watan Maris din shekarar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button