Labarai

Buhari ya kadu da harin da aka kai makarantar Sojoji ta NDA ya gargadi yan ta’addan kada su kaishi bango

Buhari ya kadu da harin da aka kai makarantar Sojoji ta NDA yayi Allah wadai sannan ya gargadi yan bindiga su shiga taitayinsu kada su kaishi bango

Daga Manuniya

Hankalin Shugaban kasa ya tashi game da harin da aka kaiwa makarantar Sojoji ta NDA a jihar Kaduna inda aka kashe wasu sojojin akayi garkuwa da wasu masu mukamin Manjo.

Buhari yayi tur da Allah wadai da wannan hari sannan ya baiwa jami’an tsaro umurni su gaggautar kubutar da sojojin da aka yi garkuwa dasu sannan su kamo yan bindigar.

Mista Buhari ya kara da gargadin yan bindiga cewa zai yi maganin su don yaga suna neman kaishi bango.

Masu karatu wannan jawabi Manuniya ce kawai ta kirkire shi domin munsan alal hakika wannan shine iya abunda ko matakin da shugaban kasar Nigeria ake ganin zai iya dauka dangane da abunda ya faru a makarantar Sojoji ta NDA idan akayi la’akari da abubuwanda suka faru a baya ko me kuke gani?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button