Addini da RayuwaLabarai

[Hotuna] El-Rufai ya kammala gina kasuwar Magani da shaguna fiye da 900

El-Rufai ya kammala gina kasuwar Magani dauke da shaguna fiye da 900 da wutar Sola 500KW

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya kammala gina kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna kuma ana sa ran bude ta domin cigaba da kasuwanci.

Manuniya ta ruwaito sabuwar kasuwar wacce aka mayar da ita ta zamani ta kunshi wutar Solar mai karfin kilowat 500KW ta Solar da shaguna fiye da 900 da kuma kanti da rumbuna kasa kaya ba adadi.

Hakazalika an gina Bankuna da ofishinyan sanda da ginin sashin gudanarwa da wajen yan kwana-kwana masu kashe gobara da kuma asibiti.

Sai kuma kwata na yanakan dabbobi da kuma manyan rumbunan da aka gina domin rika ajiye kaya. Gwamnatin jihar Kaduna ta ce a yanzu ta dukufa wajen ganin ta kammala gina sauran ragowar kasuwanni da take kan yi a fadin jihar Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button