Labarai

An shawarci Buhari ya kula da bukatun sojoji kada su tsere a fagen daga kamar na Afghanistan

An buƙaci Buhari ya kula da bukatun sojoji kada su tsere a fagen daga kamar na Afghanistan

Daga Manuniya

Wani babban farfesan masanin tarihi da sha’anin kasashen duniya dake jami’ar Lagos, Abolade Adeniji, ya buƙaci Gwamnatin tarayya ta kyautata jin dadin sojojin Nigeria dake fagen daga suna yaki da yan ta’addan Boko Haram a jihohin Borno, da Yobe, da sauran jihohin shiyyar Arewa maso gabas.

A tattaunawarsa da majiyar Manuniya, Farfesan yace kiran ya zama wajibi duba da ganin abunda ya faru a Afghanistan inda Sojojin kasar dake fagen daga suka tsere wanda hakan yayi sanadiyyar mayakan Taliban suka kwace kasar.

A don haka Farfesa Adeniji ya nemi Gwamnati ta kula wajen wadata sojojin Nigeria  da kayan aikin da suke bukata sannan a biyasu hakkokinsu akan kari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button