Labarai

Tinubu muke so a baiwa takara a 2023–inji Jiga-jigan APC daga Kudu

Daga Manuniya

Jam’iyyar APC reshen Lagos sun kekashe kasa cewa wajibi ne APC ta fitar da dan takara daga shiyyar Kudu kuma Bola Ahmed Tinubu za a baiwa takarar a 2023.

Manuniya ta ruwaito wani jigo a jam’iyy APC, Sanata Adeseye Ogunlewe, yana fadin cewa zancen da IBB yayi na cewa kada a zabi dan sama da shekara 60 zancen banza ne domin shekaru basa cikin abun dubawa game da dan takara.

Adeseye ya kara da cewa zabe a Nigeria batu ne na kudi, yan Nigeria kudi suke so, da zaran ka fitar da kudi komi zai dauki saiti kuma Tinubu yana da kudin.

A hirar sa da tashar Arise TV a safiyar yau Laraba Sanatan wanda ya rike mukamin minista ya ce duk wani jigon siyasa yaron Tinubu ne, kama daga Osinbajo, Fashola, Fayemi da sauransu kowa dan amshin shata ne sai abunda Tinubu yace, don haka yana son shugabancin kasar kuma shi suke so a tsayar a 2023.

A cewar Sanata Adeseye batun tsufa da rashin lafiyar da Tinubu ke fama dashi ba wani abun damuwa bane kowa ma yana rashin lafiya musamman idan mutum ya haura shekara 70

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button