Addini da RayuwaLabarai

Gwamna Zulum ya rusa masallatai 11 da coci 4 a Maiduguri

Gwamna Zulum ya rusa masallatai 11 da coci 4 a Maiduguri

Daga Manuniya

Kungiyar kare hakkin musulmi ta Nigeria, MURIC, ta yi fatali da farfagandar da kungiyar kiristoci ke yi cewa Gwamna Babagana Umaru Zulum nata rusa coci a jihar Borno, MURIC ta ce a binciken da tayi ta gano cewa kawo yanzu Gwamnan ya rusa masallatai 11 ne da coci 4 kacal.

Manuniya ta ruwaito cikin masallatan da Gwamnan ya rusa a karkashin hukumar raya birane ta jihar Borno wato BOGIS har da masallacin Fato Sandi dake kusa da fadar Shehun Borno a Maiduguri.

Sauran sun hada da masallatai Biyu a tsohon ginin Musami complex dake Jos road a Maiduguri. Kazalika Gwamnan ya rusa masallacin dake daura da NITEL da kuma wani masallacin a Kano Road, daura da Bulumkutu, Sannan ya rusa masallatai 1 a kusa da wani hotel a Galadima da kuma 1 bayan Timber shade, dake Baga Road.

Manuniya ta ruwaito MURIC ta kuma gano Gwamna Zulum ya rusa masallatai 5 a shatele-talen Customs round-about dake Maiduguri – Bama

Sanarwar ta shawarci kungiyar Kiristoci ta rika bincike kafin ta yi jawabin da ka iya tada zaune tsaye domin duka masallatai 11 da coci 4 da aka rushe sun saba doka ne kuma an tabbatar da hakan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button