Labarai

DA DUMI-DUMI: An kashe manya-manyan yan fashin daji 4 da suka addabi Kaduna

An samu nasarar kashe manyan yan fashin daji 4 da suka addabi Kaduna

Daga Manuniya

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce an kashe wasu jiga-jigan ‘yan fashin daji hudu da suka addabi yankunan jihar a yayin wani artabu da suka yi da sojoji.

Manuniya ta ruwaito Yan fashin dajin hudu da aka kashe sun hada da Alili Bandiro, Dayyabu Bala, Bala Nagwarjo da Sulele Bala.”

An kashe su ne a wani fitaccen tsaunin da ake kira Maikwandaraso da ke karamar hukumar Igabi

A wata sanarwa Gwamnatin Kaduna ta kuma ce an kashe wasu da yawa daga cikin yan fashin a yayin arangamar.

Gwamna Nasiru El Rufai ya nuna farin cikinsa tare da jinjinawa sojojin sama da na kasa wadanda sukayi hadin guiwa wajen kai harin da ma sairan matakan da suke dauka na fatattakar ‘yan fashin dajin daga maboyarsu musamman a jihar Kaduna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button